Bagadaza: Ba Mu Amince Da Korar Falasdinawa Da Ake Son Yi Ba

Muna Maraba Da Dage Takunkumin Da Aka Kakabawa Kasar Siriya.
17 Mayu 2025 - 22:44
Source: ABNA24
Bagadaza: Ba Mu Amince Da Korar Falasdinawa Da Ake Son Yi Ba

Yayin da sanarwar ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Syria, ta yi maraba da dage takunkumin da Amurka ta kakaba mata, tare da jaddada muhimmancin samar da mafita ta siyasa domin kawo karshen rikicin Sudan.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbaiti (as) - ABNA - ya habarta cewa: a yau ne aka kammala gudanar da taron koli na kasashen larabawa karo na 34 a birnin Bagadaza na kasar Iraqi, inda a cikin bayanin karshe ya nuna rashin amincewarsu da korar al'ummar Palastinu.

Bayanin ya kara da cewa, "Muna nanata kin amincewa da korar al'ummar Palasdinu da kuma wajabcin shigar da agajin jin kai ga zirin Gaza".

Ya kara da cewa, "Muna kira ga kasashen duniya da su matsa lamba don kawo karshen zubar da jini a Gaza," yana mai cewa "manufar taron kasashen Larabawa shi ne mu hada kan kokarinmu da cimma muradun al'ummomin yankinmu".

Yayin da sanarwar ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Syria, ta yi maraba da dage takunkumin da Amurka ta kakaba mata, tare da jaddada muhimmancin samar da mafita ta siyasa domin kawo karshen rikicin Sudan.

Al-Sudani Ya Kaddamar Da Shirin "Asusun Hadin Kai" Don Sake Gina Gaza.

A nasa bangaren, firaministan kasar Iraki Muhammed Shi'a al-Sudani ya kaddamar da shirin "Alkawarin Larabawa" na yin kwaskwarima ga tattalin arziki, yayin da ya kuma nuna cewa an kaddamar da shirin asusun hadin kai na Larabawa don sake gina Gaza.

A yayin jawabinsa a taron kolin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasashen Larabawa, Al-Sudani ya ce, "Ayyukan hadin gwiwar Larabawa hanya ce ta ci gaban kasashe, kuma albarkatun bil'adama na daga cikin muhimman kadarorinsu".

Al-Sudani ya ba da shawarar kafa wata hanya ta tantance ayyukan ci gaba, yana mai jaddada cewa, taron na raya kasa ya kasance dandalin karfafa kawancen kasashen Larabawa.

Firayim Ministan Iraki ya nuni da cewa "Gwamnatin Iraki ta kaddamar da wani kunshin gyare-gyare na kudi da ayyukan ci gaba, kuma ta tallafa wa fannin kiwon lafiya da ilimi," yayin da ya bayyana "kaddamar da shirin kawo sauyi na Larabawa anan gaba".

A yayin jawabin nasa, ya kuma tabbatar da kaddamar da shirin asusun hadin gwiwa na Larabawa don sake gina Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha